Connect with us

Labarai

Tijjaniyya sun taya Ganduje murna yayin da Ganduje zai ziyarci kaulaha

Published

on

 

Shugaban darikar Tijjaniyya na duniya Sheikh Tijjaniyya Nyass (RA) ta bakin shugaban tawagar shugabannin Tijjaniyya da su ka zo daga Kaulaha, ta kasar Senegal, domin halartar Zikirin shekara shekara da a ke gudanarwa a fadar masarautar Kano, tun shekaru 21 da su ka wuce, Sayyadi Mahy Aliyu Cisse, ya yi jan kunne ga ainihin ‘yan Darikar Tijjaniyya kan su guji gwamutsa siyasarsu da Darikar.

Ya ce siyasa daban Tijjaniyya daban. Kowannensu zaman kan sa ya ke. Ya tabbatar da cewa “Wannan Gwamna na Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje hadimi ne na wannan Darika ta mu da kuma su ‘yan Darikar. Khalifa Sheikh Tijjani Nyass ya yi min umarnin da mu isar da sakonsa na taya murna gare shi na sake dawowa kan karagar mulkin Kano.”

Ya kuma nusantar da cewa sama da shekaru 50 da su ka wuce, akwai alaka mai karfi tsakanin masarautar Kano da gidan Tijjaniyya daga Kaulaha. Ya ce “Wannan alaka ta mu ba wai yau ko yanzu ta fara ba. Dadaddiya ce kuma cikin soyayyar Allah da Manzonsa, Muhammad Bin Abdullah, Sallallahu Alaihi Wasallam.”

Ya yi wadannan jawaban ne ranar Juma’a da daddare da ya halarci cin abincin dare da gwamna Ganduje ya shiryawa wannan babbar tawaga da ta zo daga Kaulaha wajen Zikirin wannan shekara da a ka gabatar.

Shi wannan Zikirin shekara shekara din an faro shi ne daga lokacin da Kano, ba fa jihar Kano ba a matsayin jiha, ta kai shekaru dubu daya da kafuwa. Daga wancan lokacin yau shekaru 21 kenan a ka faro wannan aikin ibada na Zikirin shekara shekara. Shekarar da ta wuce a ka yi na 20. Wannan shekarar kuma a ka yi na 21.

Sayyadi Cisse ya jagoranci tawagar wacce take dauke da ‘ya’yan Sahibul Waqti, Gausuzzaman, Halifar Sheikh Ahmad Tijjani (RA), Sheikh Ibrahim Bin Abdullah Nyass Al-Kaulahi (RA). A cikin tawagar da akwai Sheikh Shafi Nyass, Sheikh Muhammad Zaynab dan Sheikh Abubakar Surunbai akwai kuma Sheikh Abubakar Sheikh Tijjani Nyass.

Shugaban tawagar ya kara da cewa “Mu a can Kaulaha kullum mun yarda da cewar abinda ya shafi Najeriya, musamman jihar Kano, to mu ma ya shafe mu. Saboda haka zaman lafiya a Kano mu ma zaman lafiya ne a wajen mu.

Saboda ganin yadda wannan bawan Allah gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ke kula da wannan Darika ta mu da mabiyanta, ya sa a wancan lokacin kafin a yi zabe mu ka dage wajen yi masa addu’ar dawowa kan mulki. Alhamdulillah yau ga shi Allah Ya kawo mu dawowarsa. Mu na kara taya ka murnan samun wannan nasara.”

Sayyadi Cisse ya ce “Wannan suna na ka na Khadimul Islam ya cancance ka matuka da gaske. Saboda ganin yadda ka ke ta yin dawainiya wajen ganin samuwar bunkasar wannan addini na Musulunci. Sannan mu na yabawa da kokarin da ka ke yi na hada kawunan Musulmi a wannan jiha mai albarka ta Kano da kuma kasa baki daya.”

Ya ce sun shaida daga Halifofin Tijjaniyya na wannan jiha da ma kasa gaba daya, yadda gwamna Ganduje ya ke tiri-tiri da su. Sa’annan ya umarci wadannan Halifofi, musamman wadanda su ke a Kano, da su kara dagewa wajen yi wa jihar addu’a ta kara bunkasa da zaman lafiya.

Dukkan Halifofin, musamman manyan gidajen Darikar Tijjaniyya da ke Kano, sun halarci wannan liyafar cin abincin dare da aka shiryawa wannan babbar tawaga.

A nasa jawabin gwamna Ganduje godiya ya yi na addu’o’in da ya ce wadannan bayin Allah su na ta yi wa wannan jiha ta Kano, har Allah Ya kara kawo dauki a ka kara samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Ya ce dukkanin ilahirin jagororin Tijjaniyya a jihar Kano su na yin iya na su kokarin wajen ganin an samu tabbatuwar zaman lafiyar jihar da kuma bunkasar tattakin arzikinta gami da ci gaban jihar gaba daya.

“Kuma in sha Allah ba da dacewa ba zan kawo ziyara ta musamman Kaulaha a kasar Senegal. Kamar yadda Shehi ya fada, dukkan abinda ya faru a Kano tamkar ya faru ne a Kaulaha. Saboda kusancin na mu ya kai matuka. Ya kai ya kawo Alhamdulillah. Mu na kara godiya ta musamman kan irin addu’o’in da a ke mana,” in ji gwamna.

Gandujen ya ambaci cewar shi wannan Zikirin shekara da ake yi, ba karamin alheri ya ke kawo wa wannan jiha ba. Ya kara da cewa “Mu na kuma kara godiya da wannan babbar alaka da a ka ci gaba da kullawa tsakaninmu. Wannan ya nuna yadda Allah Ya ke cikin wannan al’amarin na kauna da soyayya cikin Allah, saboda Shi kuma a ka fuskance Shi.”

Abba Anwar
Babban Sakataren Yada Labarai Na Gwamnan Jihar Kano
Asabar 12 ga Oktoba, 2019

Click to comment

Leave a Reply

Labarai

Ƴan Bindiga Sun Kashe Mafarauta 18 A Taraba

Published

on

Ƴan bindiga sun kashe mafarauta 18 a wani harin da suka kai a ƙaramar hukumar Bali da ke jihar Taraba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an kashe mafarautan 15 ne a wata arangama da ƴan bindiga a wani dutse kusa da garin Maihula a ranar Talata, 28 ga watan Nuwamba.

An ruwaito cewa ƴan bindigan da yawansu ya haura 200 sun yi yunƙurin kai hari a garin Bali Shalkwatar ƙaramar hukumar Bali, da wasu ƙauyukan da ke kewaye amma mafarautan sun yi artabu da su.

Ƴan bindigan waɗanda suke ɗauke da miyagun bindigu da suka fi na mafarautan, sun halaka mafarauta 15 a yayin artabun.

Wata mazaunin yankin mai suna Musa Umar ya bayyana cewa, mafarauta 14 ne suka mutu a wurin artabun, yayin da wasu mafarauta da dama suka samu raunuka, ɗaya kuma ya mutu a hanyar zuwa Asibitin Jalingo wanda adadin ya kai 15.

Shugaban kungiyar mafarauta na jihar Taraba, Adamu Dantala ya bayyana cewa an kashe mambobinsa 15 a wata arangama da ƴan bindiga.

Ya ce ƴan bindigan sun kuma yi wa mambobinsa kwanton ɓauna a kusa da garin Dakka a ƙaramar hukumar Bali inda suka kashe mafarauta uku.

 

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin Tinubu Za Ta Inganta Tsaro Da Bunƙasa Tattalin Arziƙi – Fadar Shugaban Ƙasa

Published

on

A kasafin kudin shekara mai zuwa ta 2024, Bola Ahmed Tinubu ya ce babban abin da zai dage a kai shi ne tsaro da zaman lafiya a ƙasa Najeriya.

Fadar shugaban kasa ta ce shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sha alwashin samar da ayyukan yi tare da farfado da tattalin arzikin Najeriya.

A jawabin da ya gabatar, Bola Tinubu ya ce za a yiwa tsarin tsaro kwaskwarima a Najeriya domin a tsare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Kundin kasafin kudin shekarar 2024 ya fi karkata zuwa ga wasu abubuwa takwas, kamar yadda mai magana da yawun shugaban ƙasa Ajuri Ngelale ya sanar a jiya Laraba.

Daga cikinsu akwai samar da hanyar da masu hannun jari za su kawo kudi domin yin kasuwanci wanda hakan zai inganta tattalin arziki.

Gwamnatin Tinubu za ta kara tsayawa tsayin-daka wajen yakar talauci da zarar an amince da kasafin kudin na 2024 a majalisun tarayya.

Kasafin kudin 2024 ya bada karfi a abin da ya shafi cigaban al’umma, musamman kananan yara wanda sai da su ake cigaba.

 

Continue Reading

Labarai

Ƴan Bindiga Sun Hallaka Manoma Mutane Biyu A Taraba

Published

on

Wasu da ake kyautata zaton ƴan bindiga ne sun kashe manoma biyu a gonakinsu a yankin Yangtu a jihar Taraba.

Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Talata a kudancin jihar da ke shiyyar Arewa maso Gabas.

Tsohon ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Ussa a majalisar dokokin Taraba, Habila Timothy, ya bayyana cewa manoman sun fito ne daga ƙauyen Kpambo.

Ya shaida wa gidan talabijin na Channels cewa manoman sun je gonarsu da ke Kwambai, garin da ya haɗa iyaka da ƙaramar hukumar da kuma yankin Yangtu.

A nasa ɓangaren, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar yan sandan jihar Taraba, Abdullahi Usman, ya ce har yanzu rahoton bai kai ga ofishin ƴan sanda ba.

Ya kuma ƙara ba da tabbacin cewa hukumar ta ɗauki matakai kuma an yi nisa a kokarin kakkabe yan bindiga gaba ɗaya daga jihar.

 

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: