An Rantsar da zababbun shugabannin Kungiyar Yan Jaridu Reshen Gidan Rediyon Tarayya Pyramid dake Kano.

An rantsar dasu ne karo na Biyu a gaban Wakilai daga sassa daban daban ciki har da Shugaban kungiyar Yan Jaridun jihar Kano kwamared Abbas Ibrahim Wanda Mataimakin sa kwamared Idris Zakariyya ya wakilta.
Inda ya bayyana farin cikinsa a gare su tare da jawo hankulan su akan aiki tukuru kamar yadda suka yi a zango na farko, kuma ake yaba musu.

Shima da yake gabatar da jawabinsa Shugaban Gidan Rediyon Pyramid Isma’ila Ahmad Dabai ya yaba musu matuka kasancewar yadda suke aiki don ganin an kwatowa ma’aikata hakkunannsu.

Sai da Shugaban yayi wani kira ga shugabannin da su rika Jan hankulan ma’aikantan Gidan akan Jajircewa akan ayyukan su, ba tare da ana samun sabani ba idan suka tsaya akan haka to tabbas an samu gagarumar gudunmawar wannanan kungiya daga karshe ya musu fatan alheri da kuma fatan nasara akan ayyukan da zasu tunkara.

Shima anasa jawabin zababben Shugaban kungiyar Kwamared Mustapha Gambo Muhammad ya nuna farin cikinsa game da yadda aka sake zabansu a karo na Biyu inda yayi alkawarin dorawa akan ayyukan da suka faro tun zangon farko, ya kuma tabbatar da cewa zai yi iya kokarinsa don ganin an gudanar da aiki yadda ya kamata tare da hadin gwiwar masu dafa masa da aka zabe su tare.

Wanda aka zabe su karo na farko, Wanda kuma Barrister Hamisu ya rantsar dasu tare da fara aiki nan take,
Sun hadar da:

1)Mustapha Gambo Muhammad (Shugaba)
2) Mukhtar yahya shehu(Mataimakin Shugaba)

3) Aminu Abba Kwaru (Sakatare)

4) Muhammad Adamu Abubakar( Mataimakin Sakatare)

5) Yakubu Abubakar Gwagwarwa (Ma’aji)

6) Sani Idris Mai Waya R/Lemo( Mai Bincike)

7) Shafa’atu Usamatu Mahmud( Mai kula da Kudi).

Leave a Reply

%d bloggers like this: