Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya tabbatar da tsayawa tsayin daka don ganin an kwatarwa yaran da aka sace haƙƙinsu.
Cikin wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Kano Mallam Abba Anwar ya fitar a yau, Gwamna Ganduje ya ce ya za su kira iyayen yaran da aka sace don samun cikakken bayani tare da tsayawa gaban shari a har sai aan tabbatar da adalci ga yaran da aka sace.
Ya ce za a kafa wani kwamiti da zai bi diddigI don gano masu hannu a ciki, kuma duk wamda aka samu da hannu a ciki zai ɗanɗana kuɗarsa.
Haka kuma kwamitin zai duba hanyar da ake bi wajen satar yaran ytare da cefanar da su don ganin an daƙile hanyar don gudun ƙara faruwar hakan a nan gaba.
Sannan ya shawarci iyaye da su ƙara sa ido kan ƴaƴansu don ganin an samu cikakken tsaro a jihar Kano.