Hukumar matasa yan yiwa kasa hidima ta tabbatar da cafke Wasu dake dauke da takardun kammala karatu na Bogi.

Babban Daraktan hukumar Birgediya Janar Shu’aibu Ibrahim shine ya tabbatar da hakan a lokacin da ake yiwa matasan dake Kokarin fara hidimar kasa zubin farko bitar wuni daya a garin lokoja.
Birgediya Shu’aibu yace Akalla matasa 95 aka kama dauke da shaidun kammala karatu na Bogi.

Ya kuma ce matasan guda 60 sun fito ne daga jami’oi daban daban na kasar nan, a yayin da 30 kum daga jami’oin kasashen Afrika, daban daban.
