Babbar kotun jihar kano mai lamba 8 karkashin Justice usman na Abba ta sanya ranar 14 ga watan gobe domin sauraran martani daga lauyan shugaban hukumar Karota Baffa Babba dan agundi.

Wani Lauya mai zaman kansa ne anan jihar kano barrister Rabi, u Sa,idu Rijiyar lemo ya yi karar gwamnatin kano da shugaban hukumar karota Baffa Babba Dan agundi, inda yake zargin gwamnatin kano bata bi kaidojin da kundin dokar Hukumar ba wurin nada Baffa Baffa Dan agundi
Mai karar ta bakin lauyansa barrister Abubakar Sadik Usman ya roki kotun da ta tunbuke Baffa Babba Dan agundi daga shugabancin hukumar Karota, inda ya dogara da sashi na 11 sakin layi na 2 na dokar da ta kafa hukumar karota ta shekarar 2012

Lauyan ya zaiyano mutanen da suka cancanta su shugabanci hukumar kuma a cewarsa Baffan baya cikin wadanda suka cancanta.

Lauyan da yake Kare baffa barrister M S waziri ya bayyanawa kotun cewar zai shigar da takardun suka akan ko kotun tana da hurumin jin karar, ko masu karar suna da hurumin shigar da karar shima lauyan gwamnati Abubakar Sadik ya bayyana cewar zai shigar da takardun suka.
An kuma sanya 14 ga watan gobe dan jin martanin