Hukumar Hizbah a jihar Kano ta yi Allah wadai da satar yara tara da aka yi a jihar kano.

Shugaban Hukumar Mallam Haroon Ibn Sina ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Helkwatar hukumar.

Ya ce hukumar Hizbah ta kaɗu matuƙa bisa satar yara ƙanaa da aka yi har aka sauya musu addini daga musulunci zuwa kirista.

Hukumar ta ce wannan babban abin takaici ne a ce ana satar yara a jihar kano a mai da su wata jihar har ma a sauya musu yare da suna.

Sannan Hizbah za ta samar da hanayr da za a magance ƙara faruwar hakan, a cewar kwamandan, za a bi dukkan hanyoyin da za a bi wajen ganin an shigar da aikin hizba don kula da yara a jihar Kano.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: