Wata cibiyar yaƙi da cututtuka kamar zazzaɓin cizon sauro, HIV da tari a duniya ta tabbatar da saka ɗamb wajen tallafawa jihar kano don yaƙi da zazzaɓin cizon sauro.

Shugaban cibiyar a Najeriya Dakta Ibrahim Faria ne ya tabbatar da cigaba da bada gudunmawa don yaƙar cututtuka ta hanyar rigakafi a jihar, har ma suka fara shirin aikin ta hanyar kafin alƙalami na naira biliyan 11.

Ya ce jihar Kano ce kan gaba cikin jerin jihohin Najeriya da aka gani a ƙasa wajen yaƙi da cututtuka.

Cikin sanarwar da babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Kano ya fitar a yau juma a a ya ce a yayin da suka kai ziyarar ga gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya tabbatar da cigaba da bawa fannin Lafiya ƙarfi don yaƙi da cututtuka.

Gwamna Ganduje ya bada misali da rigakafin cutar shan inna da aka ɗauki watanni bakwai ba tare da ɓullar cutar ba, ya ce wannan babbar nasara ce da jihar ta samu a fannin lafiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: