Hukumar dake yaki da masu yiwa Tattalin Arziki zagon kasa EFCC Reshen jihar kano tabbatar da kame mutane uku dake damfarar mutane miliyon kudade da sunan zasu sama musu aiki.

EFCC ta cafke mutanen ne a wani shago da suke ikirarin ofishinsu ne dake lamba 540 Ring road Eastern bypass Hotoro Kano.

Mutanen da Hukumar ta cafke sun hada da sulaiman Shariff Abdullahi, da Auwal shehu Usman, sai Mujaheed Umar Muhammad, Wanda yanzu haka hukumar ke bincike akan su daga bisani abin da bincike ya nuna sai a yanke hukuncin saki ko Kuma Mika su gaban kuliya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: