Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta tabbatar da zagaye zakin da ya kufce da nufin kamashi ko kuwa daƙile fargabarsa.Kakakin yan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya shaidawa mujallar Matashiya hakan yayin gabatar da shirin kai tsaye kan kuɓucewar riƙaƙƙen zakin.

ya ce kwararrun ƴan sanda ɗauke da bindigogi da kuma kwararrun kama namun daji ne kaɗai suka shiga cikin gidan zoo na Kano
Har yanzu babu hasarar rai ko rauni, a cewar DSP Abdullahi Haruna

