Labarai
Ƙatuwar jimina da akuyoyi biyu zakin ya cinye ko wanne lokaci daga yanzu zakin na iya farkawa – Matashiya
Kowanne lokaci daga yanzu zakin na iya farkawa, kuma yana cikin ɗakin jimina.
A yanzu haka zakin na ɗakin jimina bayan an masa allurar harbi da za ta ɗauki tsawon mintuna goma sha biyar kafin ya farka.
Ana sa rai za a kawo wata allura daga Abuja domin yi masa ita wadda za ta ɗauki awanni kafin a mayar da shi ɗakinsa.
Ku dakacemu.
Labarai
An Kone Ofishin Yan Sanda A Anambra
Wasu ƴan daga sun kai hari tare da ƙone ofishin ƴan sanda a jihar Anambra.
An kai harin ne ofishin ƴan sanda na Neni da ke ƙaramar hukumar Anaocha a jihar da misalin ƙarfe 02:00am na dare wayewar yau Alhamis.
Mai magana da yawun ƴan sanda a jihar Tochukwu Ikenga ya ce mutanen sun kai harin ne da abin fashewa da ake zargi bam ne.
Sannan ya ce maharan ba su ɗauki makaman jami’an ko yin garkuwa da jami’an su ba.
Ya ƙara da cewa, maharan sun gudu bayan da ƴan sanda su ka ci ƙarfinsu.
Zuwa yanzu ana ci gaba da hibiya don gano su waye su ka kai harin tare da kamasu.
Sai dai bai bayyana asarar da aka yi ba a sakamakon harin da aka kai.
Labarai
An Kama Ƴan Fashin Da Su Ka Yi Wa Matar Aure Fyaɗe A Jigawa
Rundunar ƴan sanda a jihar Jigawa sun kama wasu mutane uku da ake zargi da aikata fashi da makami haɗi da fyaɗe ga matar aure a jihar.
Kwamishinan ƴan sandan jihar AT Abdullahi ne ya bayyana haka yau Alhamis.
Ya ce an kama mutane uku bayan da su ka shiga gidan wani Mudan Ibrahim mazaunin ƙauyen Chori a ƙaramar hukumar Ringim tare da yi masa fashi daga bisani su ka yi wa matarsa fyaɗe.
Ƴan sandan sun samu labarin ne a ranar 17/03/2024.
Bayan zurfafa bincike, jami’an sun kama wani Umar Ibrahim, Umar Nasara, da wani Abubakar Isah dukkaninsu mazauna ƙauyen Chori a jihar.
Tuni aka ci gaba da zurfafa bincike a kai, kuma da zarar an kammala za su gurfanar da su a gaban kotu kamar yadda kwamishinan ya shaida.
A wani labarin kuma kwamishinan ya bayyana nasarar kama wasu ƴan fashi da makami, da kuma wasu da ake zargi da aikata sata a jihar.
Labarai
Malamin Makaramtar Firamare Na Kuriga Ya Mutu A Hannun Ƴan Bindiga Kafin Kuɓutar Da Dalibai
Gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani ya sha alwashin ɗaukar nauyin karatun ɗalibai 137 da aka kuɓutar daga hannun ƴan bindiga.
Ɗaliban su ne waɗanda aka yi garkuwa da ssu daga makarantar firamare ta Kuriga a jihar.
Gwamnan ya ce zai ɗauki nauyin karatun nasu ne daga matakin Firamare zuwa sakandire ƙarƙashin cibiyar Uba Sani Foundation.
Gwamnan ya bayyana haka yau Alhamis kafin mayar da ɗaliban zuwa Kuriga.
Ya ce bayan kuɓutar da su, an ɗauki lokaci domin duba lafiyarsu kafin miƙasu ga iyayensu.
Ya ce guda cikin malaman da aka yi garkuwa da su mai suna Malam Abubakar, ya rasa ransa a hannun ƴan bindigan.
A sakamakin haka, gwamnan ya ce zai ɗauki nauyin karatun ƴaƴan malamin, tare da bai wa iyalansa naira miliyan goma.
Akwai waɗanda su ka samu larurar kwakwalwa daga cikin ɗaliban da aka kuɓutar, a don haka su ka miƙasu ga kwararrun likitoci domin duba lafiyarsu.
Sannan gwamnatin ta bayar da umarnin yin wasu ayyuka a Kuriga, wamda gwamnan ya ce garin na daga cikin garuruwan da su ka fi zaman lafiya a jihar.
-
Mu shaƙata1 year ago
Kun San Ma’anar Kalmar Chiza Dani? Waƙar Da Ke Tashe A Kwanakin Nan?
-
Labarai2 months ago
Mafi Karancin Sadaki A Najeriya Ya Koma Dubu 99,241
-
Labaran ƙetare5 years ago
Wajibi ne duk wani namiji ya Auri mata Biyar ko a ɗaure shi a gidan yari— Sarkin Swaziland
-
Al'ada5 years ago
Fahimta ta a kan matsalar aure a ƙasar Hausa
-
Labarai5 years ago
Ba kwaya ƴan sandan kano suka kama ba, babu sinadarin maye a cikin maganin – NAFDAC
-
Addini4 years ago
Lokutan da ake saurin karɓar addu’a
-
Lafiya5 years ago
Menene Genotype ? Amfanin yinsa kafin Aure – Mujallar Matashiya
-
Bidiyo3 years ago
Wanene Halilu Ahmad Getso? Ƴar cikin Gida