Yayin ƙaddamar da aikin a ƙaramar hukumar Nassarawa mataimakin gwamnan jihar Kano dakta Nasiru Yusif Gawuna wanda ya samu halartar babban sakatarensa Alhaji Tijjani Ahmed ya ce aƙalla yara 28,239 ne za su rabauta da kayan makaranta kyauta .

An fara aikin bayarwar ne a makarantar firamare ta Tudun Murtala wanda aka bawa ɗalibai 631 yayin da ɗalibai maza da mata suka rabauta.
Yayin ƙaddamar da shirin shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa Alhaji Lamin Sani ya ja hankalin iyaye da su kasance masu kulawa da ilimin ƴaƴansu.

