A kwanakinnan labarin da ke yamutsa hazo har al umma ke ta ƙoƙarin yin sharhi a kai bai wuce yadda aka ga wani hoto da jarumin Adam Zango ya wallafa a shafinsa na Instagram ba.

Hoton da ke nuna yabawa da ɗaukar nauyin karatun yara da yakai sama da naira miliyan 46.

Da yawan mutane na yin raddi kan batun ciki har da masu ruwa da tsaki a cikin masana antar da ake tunanin cewar na da alaƙa da ƙut da ƙut da jarumin da ma sauran manyan jarumai.

Al amarin da ke nuni da cewa kaf masana antar babu wanda ke da maƙudan kuɗaɗen da zai iya bayarwa kyauta don ɗaukar nauyin karatun marayu kamar yadda takardar ta ƙunsa.

A binciken mujallar Matashiya kuwa bayan dogon nazari da muka yi muka hangi cewa shi fa jarumin bai faɗa cewar ya ɗauki nauyin karatun yara ba, hasali ma kalaman da ya rubuta na nuni da cewa umarni ne ga masu dama da su yi amfani da ita kwajen tallafar marayu komai ƙanƙantar sa .

Haka kuma bisa bin diddigin labarin da mujallar ta yi na ganin an samo bakin zaren mun yi ƙoƙarin jin ta bakin jarumin da nufin samun ƙwaƙƙwarar hujja don tabbatar da gaskiyar al amarin, sai dai bai samu damar ɗaga wayarmu ba, duk da cwwa a wayar da suka yi da aokin aiki Jafar Jafar ya ce shi bai yi don a sani ba saboda Allah ya yi, to amma idan haka ne me yasa ya saka takardar da aka jinjina masa a shafinsa na Instagram?

Kuma mun yi iya bakin ƙoƙarinmu wajen samo ainihin takardar shaidar biyan kuɗin daga banki amma abin ya ci tura, don duk bankin da muka tuntuɓa sai su ce ba su da labarin haka.

Adam Zango dai na yin wani al amari da ke jawo cece kuce ga al umma lokaci zuwa lokaci kamar yadda ya sha yi a baya.

Ya kan yi abu na jan hankali wanda al umma ke tunanin sai bayan sun nutsu su ga lamarin ba haka yake ba.

Mujallar Matashiya ba ta yi ƙasa a gwiwa ba mun ƙara bin diddigi daga makusantansa da nufin samun sahihancin hakan amma ba ko alamar samun hakan, kusan kowa a jikinsa cewa yake shima a shafin jarumin ya ga haka.

Haka zalika a zahirin gaskiyar abinda ke da alaƙa da haka duk mutumin da ya iya ɗaukar zunzurutun kuɗaɗe kamar haka kuma ya wallafa takardar ban girma da aka bashi ba zai ƙi bayyanawa ƴan jarida gaskiyar al amari ba.

Binciken da mujallar Matashiya ta yi ta gano cewa jarumin ya yi hakan ne don ƙara ɗaukaka da kuma tattauna batu a shafukan sada zumunta, a wani ɓangaren kuma ya yi nuni ga masu hannu da shuni cewa su kasance masu aikata alkhairi komai ƙanƙantarsa.

Batun samun bidiyon godiya kuwa daga wani wanda ya ce daga fadar masarautar zazzau yake, binciken da muka yi mun gano cewar Adam Zango na da kyakkyawar alaƙa da masarautar da ko me ya buƙata za a yi masa musamman waɗanda ke ƙasa ƙasa.

Har yanzu dai babu tabbaci ko kwakkwarar hujja ta cewa jarumin ya biya waɗannan kuɗaɗe, sai dai wani bidiyo da ke nuni da shugaban makarantar da aka biyawa yaran kuɗin makarantar ya nuna wata takarda wadda irinta ce dai jarumin ya wallafa a shafin nasa.

Wannan dai rahoto ne daga mujallar Matashiya bisa bin diddigin Abubuakar Murtala Ibrahim.

Leave a Reply

%d bloggers like this: