Kwamitin zai fara aiki ne ba tare da ɓata lokaci ba da zarar an ƙaddamar da su a ranar 31 ga watan nan
Cikin sanarwar da babban sakataren yaɗa labaran gwamman Kano Mallam Abba Anwar ya fitar a yammacinnan, Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kafa kwamitin da zai bi diddigin satar yara a Kano dun tada Shekarar 2010.
Kwamitin da aka naɗa tsohon joji wato Justis Wada Umar Rano zai jagoranta.
An kafa kwamitin ne don bin diddigi tare da tattaunawa da iyayen yaran da ƴaƴansu suka ɓata tun shekarar 2010.
A kwanannnan ne aka gano ɓatan yara da ake sacewa daga Kano ana siyar da su a jihar Anambara tare da sauya musu addini da yare.
Yara tara aka gano kuma aka cetosu bisa jagorancin kwamishinan ƴan sandan Kano CP Ahmed Ilyasu.