Bayan yara tara da rundunar ƴan sandan jihar Kano ta buɓutar daga jihar Anambara yayin da aka siyar da su aka sauya musu addini har ma da bautar da su, rundunar ƴan sandan jihar Anambara ta tabbatar da kuɓutar da wasu yara biyu da aka cefanar.
Jami in hulɗa da jama na rumdunar ƴan samdan jihar Haruma Muhammed ne ya bayyana hakan ya ce an ceto yaran ne a Akwa babban birnin Jihar.
Sai dai har yanzu ba a tabbatar da ainihin yaran da aka sato ko daga Kano aka sacesu ba.
Kwamishinan ƴan sandan jihar ya shawarci iyayen da ƴaƴansu suka ɓata da su kai bayanai cikin gaggawa don ɗaukar mataki.