Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Ganduje ya taya shugabar gidan talabijin ARTV murnar lashe zaɓen da aka gudanar nashugaban kafafen yaɗa labarai mallakin gwamnati.

An zaɓi Hajiya Sa’a Ibrahim a matsayin shugabar kafafen yaɗa labarai mallakin gwamnati wanda ta yi nasarar ɗarewa kukerar.

Cikin wata sanarwa da babban Sakataren yaɗa labaran gwamnan kano Mallam Abba Anwar ya fitar, ya ce jajircewa da kwazo ne ya kaita ga nasarar kuma ya tabbatar da cewar za ta taka rawar gani a lokacin shugabancinta.

Ganduje ya ce Hajiya Sa’a Ibrahim tana da jajircewa tare da tunanin yadda za a bunƙasa aikin jarida daidai da zamani ta yadda za a samu cigaba mara iyaka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: