A ziyarar da ministan ayyukan gona Sabo nanono karo na farko jihar sa ta kano tun bayan da aka nada shi ministan ayyukan gona ya kaddamar da cibiyar tatsar madara a kauyen Tassa Dake Karamar hukumar dawakin kudu.

Da yake jawabi a wurin kaddamar da cibiyar ministan yace wannan cibiya zai taimaka wa fulani wajen dakile matsalolin da suke fuskanta a harkar tatsar nono. Sannan kuma hakan zai inganta sana’ionsu a zamanance.
Sabo nanono yace za’a cigaba da samar da ire iren wannan cibiyoyin Tatsar madara a fadin kasar nan don inganta Tattalin Arzikin najeriya, da kuma mayar da sana’ar a zamanance.

