Shugaban kasa Muhammad Buhari ya Mika ta’aziyyarsa ga iyalai da Al’ummar jihar bauchi dama kasa baki daya kan rasuwar Hajiya Jummai Aisha Abubakar Tafawa balewa.

Shugaban ya nuna Alhini matuka kan rasuwar uwargidan Tsohon firiyar kasar nan Sir Abubakar Tafawa Balewa.
A wani kunshin sako da ya aikewa wa gwamnan bauchi Bala Muhammad a safiyar yau Muhammad Buhari ya kadu matuka da jin labarin Rasuwar, sai dai yayi fatan Allah ya jikanta tare da bawa yan Uwa hakurin rashinta inda yace rashi ne na kasa baki daya.

Hajiya Jummai Aisha ta rasu ne a a jiya lahadi a wani asibitin kudi a jihar legas.
Ta rasu tana da shekaru 85 a duniya
