Hukumar kula da tuƙi ta jihar Kano Karota Ta tabbatar da rasa wani jami inta mai suna Tijjani Adamu wanda mota ta takeshi har ya rasa ransa.

Jami in hulɗa da jama a na hukumar Nabulusi Abubakar Ƙofar Na isa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a yau.

Ya ce jami in nasu ya kama mai motar ne a daidai lokacin da ya aikata laifi, a ƙoƙarin sa na kaishi ofishinsu ne kuma mai motar ya yi tirjiya.

Nan ta ke ya tsaya inda ya ƙi tafiya sai jami in ya fito don kunce lambar motar tasa, a nan ne kuma mai motar ya bi ta kansa.

An tabbatar da rasuwar Tijjani Adamu bayan da aka kaishi asibiti a kano.

Kakakin hukumar Karota ya ja hankalin jami an nasu da su daina shiga gaban mota idan mutum ya aikata laifi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: