Al’ummar unguwar rijiyar lemo da ke maƙoftaka da wani gidan haska fina finai wato Farida Cinema sun koka a bisa yadda masu laifi ke haura musu gidaje idan jami an tsaro suka zo kamasu.
Mutanen dai sun bayyanawa mujallar Matashiya cewa gidan kallon na addabarsu da kade kade ga warin tabar wiwi kumaidan jami an tsaro suka zo kamasu suna tsallaka gidajen matan aure har ma jami an tsaron su bisu ciki don kamasu ba tare da tunanin girman laifin ba.
A kan hakan muka ji ta bakin jami in hulɗa da jama a na rundunar ƴan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna inda ya ce, hakan babban laifi ne kuma al;ummar unguwar na da damar shigar da ƙorafinsu ga baturen ƴan sandan yankin don ɗaukar matakin gaggawa.
Kuma idan har ta tabbata jami an ƴan sandan na shiga cikin gidan matan aure to la shakka suma za a hukuntasu domin sun saɓa ƙa ida.
A ƙoƙarin kawar da dukkan matsaloli ko daƙile ɓarna a jihar Kano kwamishinan ƴan sandan jihar Kano Ahmed Ilyasu na haɗa kai da al umma don magance matsalolin da ke addabar su.