Gwamnatin tarayya tace tana Shirin tsaftace kafafen yada labarai na yanar Gizo ta hanyar Kula da irin labaran da ya dace a dinga yadawa.

Ministan yada labarai da Al’adu Lai Mohammad ne ya bayyana hakan da yake ganawa da manema labarai a Abuja.
Ministan yace ba yadda za’ayi gwamnati ta zuba ido ana yada labaran da ka iya tada hargitsi a kasa.

Ya kara da cewa manufar wannan sabon tsarin shine a tsaftace hanyoyin yada labarai a fadin a Najeriya.
