Daga Mustapha Gambo

Babban Kotun Tarayya dake kano bisa jagorancin Jostis Saadatu Ibrahim Mark ta yankewa wani Henry Duru hukuncin ya biya tarar kudi Naira dubu Dari 250 saboda kamashi da aka yi yana da jabun maganin zazzabi yana kuma sauya waadin da daya kare a jikin kwalin magani
Da take yanke hukunci Jostis Saadatu ta ce jamian Hukumar kula da ingancin magunguna da Abinci ta kasa NAFDAC ne suka kama Henry Duru a shagonsa dake kasuwar sabon gari.
Tace tun a kwanakin baya da aka gurfarnar dashi ya amince da laifinsa inda kuma ya roki Kotu da tayi masa afuwa.
Bayan data kammala sauraren bayanan Lauyoyin Hukumar Nafdac da na kariya Jostis Mark ta bayyana cewar ta amince cewar Henry ya aikita lefin da ake tuhumarsa da aikatawa don haka sai ta yanke masa biyan tarar naira dubu Dari biyu da hamsin saboda laifin da ya aikita
Da yake ganawa da yanjaridu lauyan Hukumar Nafdac barrister Samson Philip Maken ya bayyana rashin gamsuwarsa ga hukuncin inda yace zai tuntubi Shugabanin hukumar NAFDAC domin daukan matakin da ya dace akan hukuncin
Lauyan yace kamata yayi Kotu ta yanke hukunci bisa dokokin tanaje tanajen Hukumar NAFDAC
Shima Shugaban Hukumar NAFDAC a kano MUHD Shaba cewa yayi jabun maganin na iya cutar da lafiyar alumma
Shi kuwa lauyan Henry Duru chief albanus Agunnanne farin ciki ya bayyana
Jostis sa,adatu ta umarci da mayar da jabun maganin da aka kama ga hukumar NAFDAC

