Yan sandan jihar Anambra sun ceto wasu yara Biyu da aka sato su daga jihar Gombe zuwa jihar Anambra.

Mutanen da ake zargi da sace yaran sun hada da Patience Opia daga Cross River, da Ejece Obi daga Anambra, sai Blessing John daga jihar Bauchi.
Da yake jawabi ga manema labarai Kwamishinan yansandan jihar Anambra John Abang yace jami’an yan sandan jihar sunyi bakin Kokarin su don ceto yaran a hannun masu Satan yaran.

A cewar mai magana da yawun Rundunar yansandan Haruna Muhammad ya tabbatar da cewa an Mika yaran hannun iyayensu.
