Rundunar yansandan jihar Anambra Tayi nasarar ceto Wasu yara Uku da aka dauke su daga jihar Anambra zuwa jihar Delta inda aka siyar dasu.

Tun a ranar 11 ga watan oktoba ne Rundunar yansandan jihar kano tayi holan Wasu yan asalin kabilar ibo da suka sace yara Tara inda suka siyar dasu a jihar Anambra tare da musanya musu sunaye da addini.
Sai gashi a yau juma’a ma Kwamishinan yansandan jihar Anambra yayi holan Wasu da aka kama su sun siyar da Yara Uku a jihar Delta.

Kakakin yansandan jihar Anambra Haruna Muhammad ya bayyana cewa zuwa yanzu ba a gano Yaran Yan asalin wane jiha bane, sai dai ya bada lambar waya don iyayen da suka rasa yayansu su tuntube shi kai tsaye ta wannan lambar08060970639 don yin bayani ko yayansu ne.

Madogara Daily Nigerian.