Cikin wata annashuwa da tabbatar da abinda ya ke magana a kai, Ministan Tsaron kasar nan, Janar Bashir Salihi Magashi (mai ritaya) ya ce “Yau dai a Kano duk wani wanda ya ce zai rigima da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje to kuwa ya na batawa kan sa lokaci ne kawai. Ba wata tantama a wannan maganar.”

Wannan gwamna, ya ci gaba da cewa “Shugaba ne da ya san mutuncin mutane, ya iya mu’amala ta mutuntaka da mutane. Ba tare da yin la’akari da matsayin mutum ba.”

Ya yi wannan furici ne a daren yau Asabar lokacin wata liyafar cin abincin dare da Gwamna Ganduje ya shiryawa duk wadanda a ka ba wa mukamai a cikin gwamnatin tarayya, a wannan karon mulkin na biyu na Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a dakin taro na “Africa House” a fadar gwamnatin jihar Kano.

Janar Magashi ya ci gaba da cewa shi gwamnan na Kano, shugaba ne nagari wanda ya san yakamata, kuma ya san menene ya dace da jama’arsa na ci gaban al’ummarsa.

Cikin wani yanayi na gamsuwa da yadda gwamnan yake tafiyar da mulkin jihar kuma, Ministan Tsaron ya ce su duka wadanda gwamnatin tarayyar ta ba su mukamai, za su hada hannu waje daya domin ganin sun tallafawa harkar cigaban jihar gaba daya, ba tare da yin kasa a gwuiwa ba kuma.

Sannan kuma a wani arashin zance da Magashin ya yi, kamar yadda kullum Gwamna Ganduje ya ke tabbatar da cewa wannan gwamnatin ta sa ba za ta yi kasa a gwuiwa ba wajen ganin an yi harkar mulkin jihar gaba daya, Ministan cewa ya yi “Ina kira ga shugabancin jam’iyya na jiha da su yi iya kokarinsu wajen ganin an tafi da kowa. Ba tare da la’akari da bangaren da mutum ya fito ba.”

Ya yi kira kuma da jama’a da su kara zama masu lura da irin mutanen da su ke bakuntar unguwanninsu ko wuraren sana’o’insu, saboda gano bata gari, wadanda kan iya zama mugaye.

Janar Magashi ya ce “Mu na rokon Allah Ya ba wa gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje nasara a tafiyar da mulkin wannan jiha ta mu, kuma abar alfaharinmu. Ayyukan cigaba da a ke ta samu a jihar Allah Ya kara dafa masa, Ya ba shi sa’a mai dorewa.”

Shi kuma a nasa bangaren Ministan Ayyukan Gona, Muhammad Sabo Nanono, wanda shi da Ministan Tsaro ne su ka wakilci duk ragowar wadanda a ka ba mukaman, cewa ya yi “Ba na tsammanin akwai jihar da a Najeriya ta samu mukamai a wannan gwamnatin sama da jihar Kano. Wannan kuwa ya nuna mana dole mu kara jajircewa wajen ganin mun fitar da Shugaban Kasa da kuma jihar kunya.”

Bayan godiya da ya yi ga Gwamna Ganduje saboda wannan girmamawa da ya yi musu, ya kara da kira ga jama’a su dage sosai wajen ganin sun ci gajiyar dukkan wasu tsare tsare da gwamnatin tarayya ta fito da su na harkar noma.

“Shi dai Shugaban kasa ya yi iya nasa kokarin. Saboda haka shawara ta rage ga mai shiga rijiya. Idan kuma mu ka yi sake damammakin da za su zo su ka kubce mana, to kar mu yi kuka da kowa sai dai kan mu,” in ji shi.

Ya yi bayanin cewa gyaran babbar kasuwar nan ta hatsi ta Dawanau, wacce ta yi shuhura a dukkanin sassan Afirka Ta Yamma, ya na da muhimmanci na gaske, har ya kara da fadin cewa “Canza mata fasali ta koma ta zamani abu ne mai matukar muhimmanci. Sannan idan ma jama’a ba su sani ba, su sani, a wannan kasuwa ta Dawanau fa, a kullum a na yin cinikin kusan na Naira Milyan Dubu Biyar.”

A nasa jawabin tun da farko, Gwamna Ganduje godiya ya yi ta musamman ga shugaba Buhari, gami da yabon manufofin tafiyar da mulkin kasa kamar yadda Shugaban kasar ya ke yi.

Ya kara da cewa “Kamar yadda mu ka sani ne, saboda tsabar yarda da yadda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ke tafiyar da mulkin kasar nan, mu ka sake ba shi wata damar a wannan karon zabensa na biyu, Kano ta sake ba shi kuri’u masu dimbin yawa.”

Ya kuma yi jawabai da yawan gaske wajen irin ayyukan cigaban kasa da gwamnatinsa ke ta bubbugowa jihar. Tare da yin kira ga jama’a da su ci gaba da marawa gwamnatin Buhari baya saboda samun ci gaban kasa.

Mutane guda 25 ne wadanda a ka yi wa wannan liyarar ta cin abincin dare da gwamnan ya shirya saboda taya su murna da kuma kara tabbatar musu da goyon bayan gwamnatinsa da jama’ar Kano gaba daya wajen ganin an kara samun dauwamammen zaman lafiya a jihar da kasar gaba daya.

ABBA Anwar
Babbar Sakataren Yada Labaran Gwamnan Jihar Kano
Asabar 2 ga Watan Nuwamba, 2019

Leave a Reply

%d bloggers like this: