Mun samu rahotanni daga fadar gwamnatin Kano cewa cikin sanarwar da babban sakataren yaɗa labaran gwaman Kano Mallam Abba Anwar ya fitar cewa, a gobe Talata gwamnan Kano Abdullahi Ganduje zai rantsar da sabbin kwamishinoninsa.
Za a rantsar da su a gobe Talata a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano.
Bayan gabatar da sunayen mutane 20 ga majalisar dokoki don tantancesu a matsayin kwamishinoni a yau.