Kungiyar kwadago ta Najeriya ta yi Kira ga Yan majalisun jihohin kasar Nan da su tsige duk gwamnan da yaki amincewa da Biyan sabon tsarin Albashi mafi karanci dubu talatin.

Babban sakataren kungiyar Emmanuel Egboaja ne ya bayyana hakan ga manema labarai a garin legas.

Inda yace kungiyar sun Mika kokensu ne ga majalisun jihohin kasar Nan akan lallai sai an tabbatar da tsarin sabon Albashi da gwamnatin Tarayya ta amince dashi.

Ta kuma bukaci muddin gwamnonin suka ki amincewa to su tsigesu daga kujerarsu kawai.

A cewar Ogboaja Gwamnonin kasar Nan basu da wani hujja da zasu ce bazasu iya Biyan sabon tsarin Albashi mafi karanci dubu talatin ba. Kawai sai dai basu yi niyya ba.

Madogara Daily Nigerian

Leave a Reply

%d bloggers like this: