Kwamishiniyar harkokin mata a kihar Kano Dakta Zahra u Muhammad Umar ta sha alwashin dakile ɗabi ar shaye shaye da ta addabi mata a jihar Kano.

Dakta Zahra u wadda ta bayyana hakan yayin da ta ziyarci ma aiƙatar karon farko batan rantsar da ita a matsayin kwamishina, ta ce samar da cigaba a fannin rayuwar mata na daga cikin manufar gwamnatin Ganduje.

Cikin sanarwar  da mai magana da yawun ma aikatar Hadiza Mustapha Namadi ta fitar, Dakta Zahra u ta ce babu shakka ɗabi ar shaye shaye ta zo ƙarshe a faɗin jihar Kano.

Yayin da ya tarbeta lokacin da ta halarci ma aikatar Babban Sakatare Auwalu Umar Sanda a shirye suke don bada dukkanin goyon baya na ganin an samar da duk wani cigaba a jihar Kano.

Dakta Zahra u ta ce hakan ba zai samu ba sai an samu goyon baya da sadaukarwar dukkanin ma aikata da sauran al aumma baki ɗaya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: