Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya tafi zuwa ƙasar Amurka inda zai gana da manyar ƴan kasuwa da ƙungiyoyi kan cigaban Ilimi da Ruwan sha.

Ganduje zai gana da ɗan kasuwa nan Aliko Ɗangote da Bill Gate da kuma wata cibiya da ke tallafawa mabuƙata.

Cikin wata sanarwa da babban sakataran yaɗa labarain gwamnan Kano Mallam Abba Anwar ya fitar, sanarwar ta ce Gwamna Ganduje ya damƙa ragamar Mulki a hannun mataimakinsa Dakta Nasiru Yusif Gawuna.

Sannan ya umarci hadiman da ya naɗa da su cigaba da gudanar da aikinsu babu ƙaƙƙautawa.

Gwamna Ganduje zai kwashe kwanaki goma a ƙasar Amuruka kuma za a maida hankali ne don tabbatar da sabon tsarin nan na bada ilimi kyauta kuma dole a jihar Kano.

Leave a Reply

%d bloggers like this: