Labarai
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta karrama shugaban mujallar Matashiya

Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano Ahmed Iliyasu ne ya bada lambar yabo ga shugaban Mujallar Matashiya da wasu ƴan jarida 17.

Ahmed Iliyasu wanda aka ɗaga darajarsa zuwa matakin AIG ya ce jajircewa da aiki tuƙuru bisa tsari ne ya sa ya karrama ƴan jaridan da kansa.

Yayin da yake jawabi jim kaɗan bayan karrama ƴan jaridun jami in hulɗa da jama na rundunar ƴan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce kwamishinan ya yaba da kwazon waɗanda aka karrama ganin irinn gudunmawar da suka bayar har aka cimma nasara zuwa wannan mataki.

Wasu daga cikin waɗanda aka karrama akwai Aminu Abdu baka noma na Freedom Radio, da Richad Okapo na jaridar Daily Trust, sai Nazifi Bala Dukawa daga Express Radio.
Sauran sune Asma u Sani daga Dala Fm da shugaban Mujallar Matashiya Abubakar Murtala Ibrahim.
Sauran sune Bashir Sharfaɗi mai rubutu a yanar gizo da Aminu Sule shima mai rubutu a shafukan sada zumunta.
Kwamishinan yaa bayyana nasarorin da ya samu daga lokacin da aka kawoshi jihar Kano a matsayin kwamishina zuwa yanzu, an samu damar kama masu daban daban ciki har da ƴan ƙungiyar Boko Haram.
Labarai
‘Yan Takarar Gwamnoni A Jam’iyyar PRP Sun Koma SDP

‘Yan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar PRP a zaben 2023 na sun sauya sheka zuwa jam’iyyar SDP.

Shugaban kungiyar ‘yan takarar gwamnan a PRP Malam Hayatuddeen Lawai Makarfi ya tabbatar da ficewarsu daga PRP zuwa SDP.
Shugaban kungiyar ya bayyana cewa sun dauki matakin koma SDP ne domin tsamo kasar nan daga halin da take ciki.

Lawai Makarfi wanda ya yi takarar gwamna a jam’iyyar ta PRP a Jihar Kaduna, ya bayyana cewa mutane na sauya sheka zuwa SDP ne bisa yadda da shugabancinta.

Makarfi ya ce sauya shekar su wani shiri ne na hadin domin kubtar da Najeriya daga shugabanci mara kyau, inda kuma ya nuna damauwarsa bisa yadda ake ci gaba da samun zubar jini, karuwar takauci, ya yin da hukumomin gwamnati ke durkushewa, inda kuma jam’iyyar APC da PDP suka mayar da mulkin kasar tamkar kasuwanci.
Kungiyar ‘yan takarar gwamnan ta kuma mika godiyarta ga PRP bisa damar da ta ba su a siyasa, inda suka ce a halin yanzu sun koma kan hanyar gaskiya.
Shugaban jam’iyyar SDP Malam Shehu Musa Gabam ya shaida musu cewa jam’iyyar za ta bai’wa masu sauya shekar dukkan wata dama da ta kamata.
Labarai
Gwamnatin Kaduna Za Ta Dauki Ma’aikatan Lafiya Sama 1,000

Gwamnatin Kaduna Jihar ta amince da daukar ma’aikatan lafiya 1,800 a fadin Jihar.

Kwamishiniyar lafiya ta Jihar Hajiya Umma Ahmad ce ta tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Alhamis.
Sanarwar ta ce gwamnatin Jihar karkashin jagorancin gwamna Malam Uba Sani za a dauki Ma’aikatan ne domin cike gurbin Ma’aikatan a dukkan cibiyoyi kiwon lafiya matakin farko na Jihar.

Sanarwar ta kara da cewa daukar Ma’aiktan hakan zai kara tabbatar da ci gaban Jihar akan matsayin da ta ke dashi a fannin kiwon lafiya matakin farko a Najeriya.

Kwamishinyar ta kuma ce daukar ma’aikatar zai kawo karshen karancin ma’aikata da ake samu a cibiyoyin kiwon lafiyar, tare da raguwar yawaitar mace-macen mata masu juna biyu da kananan yara, da kuma kara inganta lafiyar mutanen Jihar.
Acewarta a halin yanzu ana ci gaba da gyaran cibiyoyi 255 na kiwo lafiya matakin farko, yayin da za a daga martabarsu zuwa mataki na biyu, da samar da kayan aiki na zamani, tare da bayar da muhimman magunguna duk a kokarin da gwamnatin Jihar ke yi na inganta bangaren kiwon lafiya.
Kwamishinar ta kuma ce cibiyoyin za su dunga aikin duba masu cutuka daban-daban da suka hada da ciwon suga da bai yi karfi ba, hawan jini shima da bai yi karfi ba, da bayar da tallafin wajen haihuwa da dai sauransu.
Labarai
Majalisar Wakilan Za Ta Haramtawa Masu Shekaru Sama Da 60 Tsayawa Takara

Majalisar wakilan Najeriya ta tsallake karatu na biyu kan kudurin da zai haramtawa ‘yan takarar shugaban Kasa, da na gwamnan masu shekaru sama da 60 tsayawa takara.

A zaman Majalisar na yau Alhamis, da kudurin ya tsallake karatu na biyu, bayan da dan Majalisar Hon Ikeagwuonu Ugochinyere ya dauki nauyin kudurin da ke bukatar canza wasu bangarori na kudin tsarin mulkin Kasa na shekarar 1999.
Rahotanni sun bayyana cewa da zarar kudurin ya tsalle karatu na uku, kuma shugaban Kasa ya sanya hannu akansa, hakan zai sauya fasalin tsayawa takara a Kasar.

Daga cikin abubuwan da kudurin ya kunsa sun hada da, dukkan wanda ya haura shekaru 60 da haihuwa b azai tsaya takarar shugaban Kasa ba, ko gwamna a Kasar.

Sannan kuma wajibi dukkan dan takara ya kasance ya mallaki shedar digirinsa na farko a bangaren da ya fi kwarewa akai, a matsayin mafi karancin takardar karatu.
Ya yin da kuma kudin ya bukaci yin gyara a sashe na 131 na kudin tsarin mukin Kasa, na bukatar iyaknce shekaru ga kowanne dan takarar shugaban Kasa, tare da sashi na 177 ga gwamomin Jihohi.
Baya ga wannan kuduri majalisar ta kuma amince da wasu kudurori daban-daban da suka shafi ci gaban Najeriya.
-
Labarai1 year ago
Mafi Karancin Sadaki A Najeriya Ya Koma Dubu 99,241
-
Mu shaƙata2 years ago
Kun San Ma’anar Kalmar Chiza Dani? Waƙar Da Ke Tashe A Kwanakin Nan?
-
Labaran ƙetare6 years ago
Wajibi ne duk wani namiji ya Auri mata Biyar ko a ɗaure shi a gidan yari— Sarkin Swaziland
-
Al'ada6 years ago
Fahimta ta a kan matsalar aure a ƙasar Hausa
-
Labarai6 years ago
Ba kwaya ƴan sandan kano suka kama ba, babu sinadarin maye a cikin maganin – NAFDAC
-
Addini5 years ago
Lokutan da ake saurin karɓar addu’a
-
Lafiya6 years ago
Menene Genotype ? Amfanin yinsa kafin Aure – Mujallar Matashiya
-
Mata adon gari6 years ago
Sinadarin gyaran gashi – Adon Gari