Connect with us

Labarai

Satar yara a Kano – Akwai babban kuskure cikin kalaman sarkin Kano – Sunusi Ƙani

Published

on

DAGA: KHALID SUNUSI KANI
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai, mai kowa mai komai, Wanda ya bani damar yin wannan ‘yar gajeriyar fadakar wa zuwa ga Mai Martaba Sarkin Kano da dukkan daukacin Al’umma masu irin ra’ayin sa game da satar yara da ake tayi a kwaryar birnin jahar Kano.
Wanda sanin kowa ne, Allah ya bawa Mai Martaba sarki baiwar ilimin addini da na zamani. Hakan kuma yana taimaka masa wajan iya gogayya da jama’a a duk fadin duniya. Amma sau da yawa sarki yana fadar gaskiya kuma tana yiwa mutane dadi. Amma a wannan jikon Sarki ya yi maganganu masu ban mamaki da ban al’ajabi, wanda muke ganin sarki ya yi tuntuben harshe ba haka ya kamata yace ba.
Ko shakka babu, abubuwa da dama sun faru da mai martaba sarki na wajan kasa fahimtar irin ra’ayoyin shi. Wanda sau da yawa mu mukanyi uwa da makar diya wajan wayar da kan al’umma. Amma a wannan karo bama tare da sarki. Saboda yaci karo da tsarin mu’amalar rayuwa dama tsarin koyarwa ta addinin musulunci.
Sanin kowa ne Annabi(S.A.W) yana fada a cikin wani sahihin hadisi yana cewe ” Musulmi ya fadawa dan uwansa Musulmi magana me dadi sadaka CE”. Ni na dauka mai martaba sarki zai fada musu maganganu masu nutsar da zuciya, ba kalaman da za su sa iyayen yara jimami ba.
Mai martaba sarki ya kamata yasan akwai bambanci tsakanin ‘Ya ‘yan talakawa da ‘Ya ‘yan masu kudi. A cikin talakawan ‘Ya yan su suna zuwa makarantu kama daga na BOKO zuwa na islama. Wanda sau da yawa yaran nan da Kansu suke tattaki zuwa wadan can makarantu sabanin abun yadda yake a gidan masu hannu da shuni.
Ni dinnan zan iya tuno sadda muna yara muke zuwa marantar firamare da islamiyya a kafa. Wanda muke tafiyar kimanin kilomita shida (6) zuwa da dawo wa. Amma tun a lokacin ‘Ya ‘Yan masu kudi a mota ake kaisu. Saboda haka babu yadda shugaba zai zargi iyaye da laifin barin yara suna fita daga gida. Ko kadan yin hakan ba dai dai bane.
Maganar da me girma sarki yayi ka iya tsunduma iyayen yara su fada zuwa cutar damuwa da tunanunnuka (wato depression). Wanda ba karamar illa bace a garesu.
Amma inason mai karatu ya fuskanci zance na ba ina nuna iyayen yara basu da laifi ba. Suma iyayen yara ya zama dole su kula da ‘Ya ‘yan su sosai.
Muna kira ga mai martaba sarki da ya yi gaggawar bawa jama’ar jihar Kano hakuri musamman iyayen yaran da suka salwanta.
Allah ya bayyana mana su, Allah ya kiyaye gaba, ameeen.
52ND SUG PRESIDENT BUK
LEVEL 600 MEDICAL STUDENT.

Click to comment

Leave a Reply

Labarai

Iyayen Ɗaliban Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Jami’ar Tarayya Da ke Gusau Sun Gudanar Da Zanga-Zanga

Published

on

Iyayen dalibai matan da aka yi garkuwa da su a jami’ar tarayya da ke garin Gusau da ke Jihar Zamfara sun gudanar da zanga-zangar lumana a gidan gwamnatin Jihar.

Iyayen sun yi zanga-zangar ne domin neman a gaggauta sako musu ‘ya’yansu da masu garkuwa suka yi garkuwa dasu a cikin Jami’ar.

Masu zanga-zangar sun kuma nemi da gwamnan Jihar Dauda Lawal Dare da sauran hukumomin tsaron Jihar da su yi duk mai yuwuwa wajen ganin an kubtar da ‘ya’yannasu cikin koshin lafiya.

Kazalika sun ce ‘yan bindigar sun neme wasu daga cikin iyayen daliban kan cewa ba za su sako daliban ba harsai sun tattàuna da gwamnatin Jihar.

Inda suka nemi da gwamnatin ta yi duk mai yuwuwa wajen ganin an ceto ragowar wadanda ke hannun batagarin.

Masu garkuwar, sun yi garkuwa da daliban ne tun a ranar 22 ga watan Shekarar da mu ke ciki inda suka yi garkuwa da dalibai Mata 24 da wasu ma’aikata 10 a cikin Jami’ar, a lokacin da suka kai hari garin sabon Gida garin da dakunan kwana daliban suke.

Amma bayan garkuwa da daliban jami’an tsaro sun kubtar da dalibai 13 daga cikinsu Leburori Biyu, yayin da ragowar ke hannun maharan.

 

 

Continue Reading

Labarai

Gwamna Uba Sani Ya Bayar Da Umarnin Yin Bincike Kan Harin Bom Ɗin Da Ya Kashe Masu Taron Maulidi A Kaduna

Published

on

Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya bayar da umarnin gudanar da bincike akan hallaka mutane da dama da jirgin yakin sojin Najeriya ya yi a Jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya fitar, tare da mika sakon jaje ga al’ummar Jihar.

Uba Sani ya ce gwamnatinsa ta kuduri aniyar daukar matakin kaucewa kara faruwar hakan.

Gwamnan ya kuma bai’wa al’ummar Jihar tabbacin cewa za a tabbatar da tsaro, da bai’wa mutanen Jihar Kariya a lokacin da ake kokarin kawar da ‘yan ta’adda da sauran batagari a Jihar.

Gwamna Uba Sani ya bayar da umarnin kwashe wadanda suka jikkata zuwa asibitin koyarwa na Barau Dikko, domin ba su kulawar gaggawa da kuma daukar nauyinsu.

Jirgin ya hallaka mutanen a ranar Lahadi, a lokacin da suke tsaka da gudanar da bikin Mauludin a karamar Igabi ta Jihar bayan sanya musu bom da jirgin yayi har sau biyu.

 

 

Continue Reading

Labarai

Shugaba Tinubu Ya Umarci A Yi Bincike Kan Harin Sojojin Da Ya Kashe Mutane A Kaduna

Published

on

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da bincike akan mutanen da jirgin yakin sojin sama ya hallaka a Jihar Kaduna a lokacin da suke gudanar da taron mauludi a yankin Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi ta Jihar.

Shugaban ya bayar da umarnin ne a safiyar yau Talata, kamar yadda wata sanarwa da mai magana da yawunsa Ajuri Ngelale ya fitar.

Tinubu ya nuna alhininsa akan lamarin tare da mika sakon ta’aziyyarsa ga gwamnatin Jihar da ‘yan uwa da iyalan wadanda suka rasa rayukansu.

Sanarwar ta ce shugaban ya bayar da umarnin a gudanar da bincike da kuma bai’wa wadanda suka jikkata kulawa ta musamman.

Tinubu ya kuma bukaci da mutane su bai’wa jami’an tsaron hadin kai wajen gudanar da bincike.

Sannan Tinubu yayi addu’ar neman gafara da rahmar Allah ga wadanda suka rasa rayukansu.

 

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: