Kwamishiniyar harkokin mata da samar da cigaba a jihar Kano Dakta Zahra u Muhammad Umar ta sha alwashin daƙile yawan mace macen aure da ya yawaita a jihar Kano.

Yayin zantawarta da mujallar Matashiya, Dakta Zahra ta ce yawan mutuwar aure ne jigon rashin tarbiyya da ke wanzuwa a faɗin jihar kuma za su bi duk hanyoyin da ya kamata don ganin an magance matsalar.

Ta ce babu shakka akwai matsaloli da yawa amma uwa uba bai wuce mutuwar aure ba saboda shi ne tuahen rugujewar tarbiyyar yara ƙanana da matasa.

Dakta Zahra ta ce za su yi amfani da masana wajen wayar da kai ga ma aurata tare da mutanen da suka kware wajen gyaran tarbiyya don magance matsalar baki ɗaya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: