Daga Jamila Sulaiman Aliyu

Hukumar hisbah ta jihar kano ta jihar kano tayi nasarar kame wasu Yan,uwa mata da take zarginsu da ayyukan badala.

Mataimakin Kwamandan hukumar a bangaren ayyukan musamman Mallam Shehu Tasiu Ishaq shine ya bayyana hakan ga manema labarai inda yace an Kama yan matan ne a yankin unguwannin nassarawa da kuma sabon gari.

Mataimakin Kwamanda yace hukumar Hisbah tana Kara kiran iyaye da babbar murya dan su baiwa yayan su kulawar da ta kamata take hanyar nusar dasu irin hadarin da ka iya riskar su matukar basu kaucewa MA,a,mala da maza ba.

Mallam shehu tasi,u yace idan har iyaye basu taimakawa hukumar ba to ba lallai bane a haifi da mai idanu ba.

A yayin zantawar sa da Mujallar matashiya ya sha alwashin cigaba dayin samame a matsayin hukumar Hisbah ta jihar Kano.

Leave a Reply

%d bloggers like this: