Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya amince da bayar da tallafi na naira dubu 30 ga masu yin bara a kan titi.
A ƙoƙarin gwammnatin na hana yin bara a jihar, a garin Maiduguri da Jere za a bawa matasan da suke da larura ta zahiri da adadinsu ya kai 2,862 naira dubu talatin har tsawon watanni shida.
Adadin kuɗi naira miliyan 384 gwamnatin ta ware don shirin daƙile bara a jihar.
Kwamishinan ma aikatar rage yawan talauci a jihar Nuhu Clark ne ya bayyanawa manema labarai haka.
Mutanen da aka tantance da suka kai 3,127, wasu daga cikinsu sun fara amfana tun watanni biyu da suka wuce.