Rundunar yansandan jihar Kano sun yi nasarar ceto wani yaro Dan shekaru 4 Mai suna Abdurrahman Dalha Wanda akayi garkuwa dashi.
Yan sandan sun cafke Anas Isah dan shekaru 22 da umar Hassan Mai shekaru 40 bisa zargin su day sace yaro tare da neman Kudin Fansa naira Miliyan 4 kafin su saki yaron.
Yan sandan kan kace kwabo (operation Puff Adder) sun yi nasarar ceto yaron cikin koshin lafiya a kauyen Inusawa dake Karamar Hukumar Ungogo.
Yanzu haka dai Rundunar yansandan suna bincike akansu wanda da zarar an kammala za’a gurfanar dasu gaban shari’a kamar yadda Kakakin Yansandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana hakan a cikin kunshin sanarwa da ya aikewa wa manema labarai a madadin Kwamishinan Yan sanda.