Daga Aliyu Sufyan Alhassan

Kowacce Jiha a kasar nan na da tsarin gudanarwarta ta fannoni da dama, ta bangaren zamantakewa da zuwa da tsari da Jihar zatayi tunkaho na gwada kwanji.

Nasan zakuyi mamakin mabudin rubutuna akan AMFANI KO RASHIN ALFANUN HUKUMAR KAROTA A Jihar Kano, Hukuma ce wadda tsohon Gwamnan Kano Dr Rabi’u Musa Kwankwaso ya kirkirota ta hanyar kwaikwaiyo makamanciyar hukumar da ke kula da tituna ta Jihar Ikko wato LAROTA.

Ayyukan wannan hukuma musamman anan kano shine; kula da tituna, magance haddura,da kuma motocin da suke lodi ba bisa ka’ida ba, da ma kula da motocin da suke shigowa daga wasu Jihohin don tabbatar da zaman lafiyar Jihar Kano da gudanar da rage cunkoson ababan hawa a Jihar da ta fi kowacce yawan al’umma da kuma ababan hawa.

A jihar Kano hukumar KAROTA a kiyasi tana da ma’aikata kimanin mutum 2,400 wadanda matasane da shekarunsu basu wuce daga 23 zuwa 40 ba, kuma dukkaninsu ‘yan asalin Jiha ne wadanda aka rage yawan matasa da basu da aikin yi.

A kwanakin baya Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bada damar sake daukar matasa masu matukar yawa a hukumar, sannan bayan nada Hon Baffa Baffa DanAgundi hukumar ta canja salon gudanarwarta ta gudanar da Basani-Ba Sabo domin bin ka’idar hanyoyi musamman don gudun hadura da ka iya zama ruwan dare a kano.

Hukumar a kwanakin baya ta samu nasarar gano wata mota cike da kwayoyi na bogi, wanda aka shigo da ita daga wata jiha a kasar nan, kiyasi ya nuna kusan magungunan na bogi sun kai Naira Miliyan 50 ko sama da haka, wanda dubban ‘yan asalin Kano idan sukayi amfani da wannan magani zasu iya kamuwa da cutar da ko dai ta zama ajalinsu, ko kuma kamuwa da cutar da warkewarta sai an sha wahala.

Matukar wannan hukuma na gudanar da irin wannan hukuma na gudanar da irin wannan aiki, me zai saka Kanawa suna kallonsu a matsayin BARAZANA ga masu amfani da ababan hawa? Mai Zai saka Kanawa bazasu kalli kokarin da Kannenmu, yayyenmu, sukeyi don guduwa tare mu tsira tare.

A kwanakin baya guda cikin matasa a KAROTA ya rasa ransa akan titin zuwa Airport, kuma a kokarinsa don ganin ya bi ka’idar aikinsa, sannan wani matashin shima Dan KAROTA a kwanaki biyu ya rasa ransa a kan Shatale-Talen NNPC dake Hotoro biyo bayan takeshi da wani dan Tirela yayi, shin wannan ba abun tambaya akai? Me yake Faruwa kannenmu suke rasa ransu a wannan aiki?

Na tattauna sosai da mutane daban-daban, inda kusan abin na faruwa ne ga rashin bin ka’idojin hanya da masu motoci, babura, da sauran ababan hawa ke yi a nan Kano, wanda kuma suna daukar ‘yan Karota a matsayin makiya wanda suke zaluntarsu, na tabbata idan kabi ka’idar hanya babu wani dan karota da zai nufeka da wata magana ta cewar ka taka doka.

Ya kamata KANAWA mu waye, mu sani cewar zaman lafiyar mu shine mu yi biyayya ga dukkanin dokar da aka gindaya mana, domin mu zama abin kwatance.

Na tabbata a misali a janye ‘yan KAROTA a Kano na wuni guda, Wallahi sai duk mai hawa abin hawa ya gane kurensa sakamakon irin gudunmawa da suke bayarwa akan manyan tituna, zaka tausaya musu idan hanyar Dan-Agundi, Bata, Bairut Road, ko kuma hanyar zuwa Kurna ta yadda suke kokari, komai ruwa, komai rana, komai wahala, amma bama gode musu sai dai mu nemi rayuwarsu, to ya kamata Gwamnati ta dau mataki mai karfi ga wanda yake cin zarafin yan karota musamman idan sun yi kokarin kawo gyara a aikinsu.

‘Yan Adaidaita sahu, masu hayis, da masu motocin amfani yau da kullum, mu baiwa ‘Yan karota hadin kai, wallahi ba karamin taimakawa al’umma suke yi ba, mu tsaya muyi tunani, kada son zuciya mu dinga kallonsu a matsayin makiya.

Kira ga shugaban hukumar KAROTA Hon Baffa Babba Dan-Agundi wannan kalubale ne akanka na kokarin fijiro da dabaru, hanyoyi, da salon da yaranka zasu sani wajen tunkarar wanda ya aikata laifi, sannan a dinga shirya musu Bita wanda kwararru zasu dinga jagoranta don kannenmu su sami kwarewa mai girma wajen ayyukansu.

Masha Allah, Allah ka zaunar da Kanon mu lafiya, ka baiwa shugabanninmu damar gudanar da adalci a tsakaninmu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: