Kwamishinan yansandan jihar Kano ya ce Rundunar yansandan jihar zata fara aiwatar da dabarun yaki bata gari a fadin jihar Kano.

Sabon Kwamishinan yansandan jihar Kano CP Habu Ahmadu Sani shine yayi wannan jawabi a safiyar Litinin a lokacin da yake ganawa da manema labarai.
CP Habu yace Rundunar zata gangamin wayar da Kan Al’umma Kan Illar shaye shaye da Daba tare da manyan Laifuka a tsakanin Al’umma.

Ya kuma kara da cewa Rundunar zata gudanar da gangamin ne a Makarantu, kasuwanni, da unguwannin jihar kano, da kuma aiki da kafafen yada labarai da Kafafen sada zumunta wajen gudanar aikin Rundunar.

Daga karshe Kwamishinan yansandan ya bayyana cewa akwai hanyoyin isar da sakonni ko bayanai da Rundunar zata rika karba daga bakunan Al’umma.