Hukumar gudanarwar makarantar Fasaha dake jihar Delta (Polytechnic) ta haramtawa dalibai amfani da Hula Fecin Cap (Hana sallah) a cikin makarantar.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya rawaito cewa Shugaban ne Job Akpodiete shine ya bada umarnin haramcin sanya hular jim kadan bayan an kona Huluna 500 da aka kwacewa daliban makarantar.
Mr Akpodiete Wanda Shugaban sashin walwalar dalibai ya wakilta Thomas Ojuye yace wannan haramcin na matsayin Dora daliban kan su rika shigar kamala a cikin makarantar.

Haka zalika ya kuma Kira ga daliban dasu da su mutunta dokar makarantar don zama dalibai na gari masu da’a da shigar kamala.
