Kungiyar gwamnonin jami’ar APC ta zabi gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje a matsayin gwamnan da ya fi sauran gwamnonin Kawo Ayyukan cigaban Al’umma, inda ta doke sauran gwamnonin.

Jihar Kano ta lashe kambun ne watanni biyu a jere.
Cikin wata wasika da Da babban darakatan Yada labarai na Shugaban inuwar Gwamnonin jam’iyar APC Salihu Mohammad Lukman ya fitar,

Ya bayyana cewa gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya samu wannan yabo ne sakamakon manyan ayyukan inganta rayuwar Al’umma guda 19 da ya gabatar Wanda Suka hada da, koyar da sana’oi, Samar da ayyuka, bayar da kulawa da kiwon lafiya, Inganta ilimi, Tsaro, Inganta hanyoyin sufuri, Lantarki, muhalli, Wasanni da Sauransu.

Jihar da ke biye Mata kuwa a fannin inganta rayuwar Al’umma shine jihar Legas,da yake da 18, jihar Ekiti da ya samu kaso 17, Edo 13, Katsina da Kwara 11, inda jihar Yobe da Jigawa Suka samu kaso 11,
Yayin da jihar Kaduna, Niger da Ogun suke da kaso 7.
Ita kuwa jihar Borno da yobe sun samu kaso 6, a bangare guda kuma jihohin Osun da plateau Suka samu kaso 5.
Jihohin karshe sune Gombe da kogi sai nasarrawa da Ondo suka samu Kaso 4.
A cikin Watanni biyu jihar Kano itace tafi gudanar da ayyukan da suka shafi cigaban Al’umma.