Idan ba a manta ba a kwananan ne Hukumar da ke lura da zirga zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA ta kame wani kayan maye samfurin Sholisho katan Dari da hamsin da bakwai a wani gida da ke kan titin Emir a unguwar Sabon gari da ke Kano.

Wanda kudin sa ya Kai Miliyan ashirin.
Idan ba a manta ba a kwanan baya ma hukumar ta kama wasu kwayoyin magani da ake zargin marasa kyau ne.

Mujallar Matashiya ta nemi jin ta bakin Hukumar Karota kan tana da alhakin kame kayan shaye- Shaye.

Wannan kamen kayan maye da hukumar Karota tayi na daya daga cikin ayyukanta na Binciken ababen hawa tare da gano irin nau’in kayan da aka shigo dasu jihar Kano.
Kamar yadda jami’in hulda da jama’a na hukumar KAROTA Nablisi Abubakar Ahmad ya ce hukumar karota na cikin jami’an hadin gwiwa dake yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi a jihar Kano.
Nablisi yayi Kira ga Al’umma da su rika sa idanu akan irin kayan da ake shigo dasu tare da Kai rahoto ga jami’an tsaro.