Wata Kotun Garin Maryland dake kasar Amurka ta wanke wasu mutane 3 da aka daure su tsawon shekaru 36 bisa kamasu da laifin kashe wani yaro Mai shekaru 14 a duniya.

Sai gashi an samo wasu hujjoji dake nuni da cewa wadannan mutane basu suka kashe yaron ba, kuma kotu ta gamsu da hujjojin da aka gabatar nan take kotu ta bada umarnin sakin mutanen, bayan zaman da sukayi a kurkuku na shekaru 36.
Zuwa yanzu dai ba’a bayyana adadin diyyar da za’a basu ba dangane da daurin da suka sha ba tare da aikata laifin komai ba.

