Shahararren Dan kasuwan nan Dan asalin jihar Kano, kuma Mai kudin Afrika Alhaji Aliko Dangote ya ce zai hada hannu da gwamnatin jihar Kano wajen habbaka cibiyar koyar da sana’oi a jihar Kano.

Dangote ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar bazata cibiyar koyar da sana’oi da gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya Gina a titin zaria.
Cikin wata sanarwa da babban darakatan Yada labarai na jihar kanoAmeen K yassar Ya fitar yace Dangote yayi farin ciki matuka da ganin irin kayan koyon sana’oi da aka zuba a cibiyar.

Inda yace manufofin Ganduje yayi dai dai da Nashi na kawo cigaba tare da Samar da ayyukan yi a tsakanin matasan Najeriya.
