Rundunar ƴan sandan jihar Kaɓi bisa jagorancin kwamishinan ƴan sandan jihar Habu A Sani ta yi nasarar kama wasu da ake zqrgi da garkuwa da mutane tare da kuɓutar da mutum ɗaya.

A yayin da yake holen mutanen da aka kama Wanda ya gudana a harabar helkwatar rundunar da ke Bompai,  kwamishinan ƴan sandan jihar Habu A Sani ya ce rundunar ta kama wasu da ake zargi da satar ababen hawa har ma ta kuɓutar da babur mai ƙafa uku wato Adaidaita sahu da aka sata a Kano aka kaishi jihar Zamfara.

Haka kuma rundunar ta kuɓutar da wata waya da aka sata da ƙimar kuɗinta ya kai naira 240,000.

Sannan rundunar ta kama ƴan daba sama da saba in tare da makamai daban daban ciki har da wata bindiga ƙirar hannu.

Kwamishinan ƴan sanda na Kano Habu A Sani ya shawarci al ummar jihar Kano da su cigaba da bada haɗin kai don cigaba da samar da zaman lafiya a jihar

Leave a Reply

%d bloggers like this: