Lamarin dai ya faru ne a yammacin jiya laraba, inda takaddama ta kaure tsakanin wani Mai mota da Mai babur din adaidata sahu, sakamakon Mai babur din ya goge masa goma.

Sai suka tsaya a bakin bankin Union dake Niger Road a Kano,
Nan take Dan sandan dake Gadi a bankin ya fito a lokacin da yaga takaddamar tayi tsamari, shine ya fito yace su matsa gaba kasancewar ba’a tsayawa a bakin banki.

Nan take Mai motan ya shiga zai gyara motar daga bakin bankin,
Shi kuwa Dan sandan ya daga bindiga ya harbeshi Wanda harsashi ya fasa glass din motar ya sameshi a wuya, a zatonshi wai mutumin guduwa zai yi.

Kakakin Yansandan jihar Kano SP Haruna Abdullahi Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin Inda yace tuni aka kama Dan sandan inda ake cigaba da bincike akan sa.
Ya kuma tabbatar da cewa an garzaya da mutumin asibitin malam Aminu Kano inda aka tabbatar da mutuwarsa.
Madogara
Arewa radio.