Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta karyata rade-radin da ake yadawa a kafafan sada zumunta na cewa sun cafke wata matashiya mai suna Zainab Nasir.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya shaidawa Mujallar Matashiya cewa ko kadan basu cafke wata Zainab ba, sabanin yadda ake yadawa a kafafan sada zumunta.

Ya kara da cewa wannan batu yazo akan gaba domin kuwa tuni kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, CP. Habu Ahmed Sani ya bude sabon sashe da yake bibiya tare da daukar mataki kan laifukan da ake aikatawa ta kafafan sada zumunta.

Sannan bugu da kari babban laifi ne mutum ya bada sanarwa a madadin ‘yan sanda cewa sun kama wane alhalin basu kama shi ba.

A karshe yayi kira ga al’umma da suyi watsi da wannan labarin, kuma da zarar sun kammala bincike zasu dauki mataki akai.

Da safiyar yau Jumu’a ne dai aka samu bullar wani rubuto a kafafan sada zumunta wanda ke cewa jami’an ‘yan sanda sun cafke wata fitacciyar ‘yar gwagwarmaya wato Zainab Nasir

Labarai masu alaka:

Ƴan sanda a Kano sun kama masu garkuwa da mutane shida tare da kuɓutar da mutum ɗaya

Kotu ta bayyana ranar Da zata yanke hukunci na karshe akan Maryam Sanda

Leave a Reply

%d bloggers like this: