Shugaba dole ya kasance Mai gaskiya a tsakanin Al’umma kafin ya zama Shugaba.

Dan Majalisar Mai wakiltar Zaria a Majalisar Jihar kaduna
Hon Suleman Ibrahim Dabo, shine ya bayyna hakan yayin taron lackar da
Kungiyar Daliban Zaria ( NAZAS)ta gudanar na shekarar 2019.

Taron bana Mai taken Samar da Cigaba a tsakanin Al’umma.

Taron ya gudana ne a dakin taro na Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar dake Kwalejin Barewa a Garin Zaria.

A cewarsa muddin aka samu jajirtattun Matasa to dole ne a samu shugabanni nagari.

Muddin aka samu sabanin haka to kullum zamu kasance ne a yadda muke musamman a Najeriya.

Cikin Wayanda suka gabatar da mukalar sun hada da Barrister Aysha Ahmad Muhammmad Wanda tayi jawabi akan Muhimmacin Ilimin Yara Mata.

Daga bisani Mal Umar Yakubu ya gabatar da mukala akan Tsaro da zamanLafiya a tsakanin Al’umma.

Jawabinsa ya bayyana cewa Rashin sanin inda mutum ya dosa a Rayuwa shine babban matsalar tsaro, Rashin aikin yi, da Rashin Karatu duk su suke janyo matsalolin tsaro da ake fuskanta a Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: