Kamar yadda dokar Sashi na (2) (g) da Sashi nabe5 (1)(2) ta bawa gwamnan jihar Kano damar nada Shugaban Majalisar Sarkuna don haka gwamnati ta zabi Sarkin Kano Muhammmad sunusi ll a matsayin Shugaban Majalisar Sarkunan jihar Kano.

Tun bayan da sabon dokar da gwamnatin jihar Kano tayi na kirkirar sabbin masarautu 4 a jihar.

Ganduje ya bayyana zaben Sarkin kano ne a kunshin bayani da babban sakatare yada labarai na gwamnan Abba Anwar ya fitar a jiya.

Inda gwamnan ya tabbatar wa Al’ummar jihar Kano cewa kirkirar sabbin masarautun zai taimaka wajen habbaka Tattalin Arziki jihar Kano da Samar da cigaba a fadin jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: