Masarautar jihar Kano ta bayyana cewa har yanzu bata karbi kwafin wasika daga fadar gwamnatin Kano ba na cewa an zabi Sarkin Kano Muhammmad sunusi ll a matsayin Shugaban sarakunan jihar Kano.

A cewar masarautar ita taga labaran na yawo a kafafen sada zumunta dama wasu kafafen yada labarai.
Amma basu karbi Sako a hukumance ba.

Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya nada sarkin kano A mastsayin Shugaban sarakunan jihar Kano,

Amma zuwa yanzu basu karbi sakon dake nuna wannan zabe ba kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito