Ƙungiyar masu tuƙa babur mai ƙafa uku a Kano wanda aka fi sani da Adaidaita sahu za su shiga yajin aiki daga gobe juma a.

Cikin wata takarda da ƙungiyar ke rarrabawa ga ƴaƴanta, ƙungiyar ta ce za ta shiga yajin aikin ne don samun damar tattaunawa da gwamnati a bisa tsarin harajin da ta samar.
Hukumar kula da tuƙi ta jihar Kano KAROTA ce ta sanar da fara biyan haraji ga ƴan Adaidaita sahun wanda ya haura naira dubu talatin.


Cikin sabbin tsarin hukumar, ta ce masu Adaidaita sahun za su ke sabunta takardun ababen hawansu tare da lasisin tuƙi, kuɗin da ƙungiyar ke ganin ya yi yawa har ma ta umarci ƴaƴan nata da su shiga yajin aikin daga gobe Juma a har sai an cimma matsaya da gwamnati.