Rahoto
Da yawan masu Baburan Adaidata sahu basu fito aiki ba duk da janye yajin aikin da akayi a daren jiya


Yajin aikin da masu Babura Mai kafa uku suka dauki niyar tsunduma a safiyar yau da alamun karbuwa an karbe shi.

Duk da yadda akayi sulhu na janye Kudaden da zasu biya lokaci guda.
Sai dai da alamu mafi yawa basu gamsu da irin matakin da Shugaban karota Baffa Babba dan agundi yayi ba, tare da amincewar Shugabanninsu.

Na cewa zasu biya 8000 na tracker zuwa karshen Disamba, daga bisani su biya
Su biya dubu 21.

Sai dai mujallar matashiya tayi kwarya kwarya zagaye don ganin yanayin Hada hadar Baburan Adaidata sahu akan titina.

Matashiya ta lura da karancin su akan titina haka zalika dai daikun dakeWayanda suke wucewa suna dauke ne ganye a jikin baburan Wanda hakan ke nuni da suna yajin aiki.
Wakilin Mujallar matashiya Ahmad Haysam ya zagaya wasu titina don jin Ra’ayoyin masu baburan Adaidata a lokacin da ta iskesu suna zaune inda wani Mai suna Yusuf yace bai ga dalilin da zai yi aiki a wannanan yanayin da ake ciki ba na takura. Don haka shi ya ajjiye babur dinshi har Sai baba ta gani.

Shima wani Mai suna Aminu cewa yayi rashin fitowa aiki shine masalarsu a Yanzu, kasancewa yadda gwamnati ke neman hanasu gudanar da sana’oi nsu.
Sai dai tun a daren jiya Shugabannin kungiyar Masu baburan Adaidata sahu suka Kira mambobinsu dasu bada hadin kai wajen baya gwamnati goyon baya akan kudirunsu.
Rahoto
Dala Bilayan 12 ake asara a Najeriya Sakamakon Rikicin Makiyaya da Manoma


An samu rahoton asarar akalla dala biliyan 12 a Nijeriya, sakamakon rikicin manoma da makiyaya da ya mamaye sassa daban daban na kasar.

Daraktan kungiyar sa kai ta Mercy Corps, Ndubisi Anyanwu,ne ya sanar da hakan a ranar Talata a zantawarsa da manema labarai jim kadan bayan ganawa da jami’an gwamnati a garin Makurdi.
“a cewarsa sun yi kiyasin asarar akalla $12b a kowacce shekara sakamakon rikicin makiyaya da manoma. “Wannan wani babban al’amari ne kuma da zai iya shafar kasar baki daya,”

Anyanwu ya kara da cewa akwai bukatar a mayar da hankali kan rikici tsakanin makiyaya da manoma, yana mai cewa wannan ne ma dalilin da yasa kungiyar ta shiga cikin lamarin.

Ya yi nuni da cewa kungiyar Mercy Corps, da aka samar da ita karkashin hukumar USAID, ta mayar da hankali kan gina zaman lafiya na watanni 60 a Benue da wasu jihohin jihar.

Tun farko, shugabannin kananan hukumomi a jawabansu daban daban sun lissafa rashin aikin yi, rashin ababen more rayuwa daga cikin dalilan haddasa rikicin makiyaya da manoma.

Rahoto
An samu asarar rayuka 415 a Najeriya daga watan Yuli zuwa yanzu


Wasu Alkaluman bincike na nuni da cewar akalla mutane 415 aka kashe a Najeriya a watan Yulin da ya gabata sakamakon hare hare da kuma tashin hankalin da ake cigaba da samu a cikin kasar.

Rfi hausa ta rawaito cewa Wata kungiya da ta kira kan ta ‘Nigeria Mourn’ tace an fi samun kashe kashen dake da nasaba da hare haren Yan bindiga da rikicin yan tada kayar baya da kuma barayin shanu ne a Jihohin Kaduna da Borno da Katsina.
Alkaluman kungiyar sun ce daga cikin Jihohi 21 da aka kashe mutane 415, Jihar Kaduna ke sahun gaba da mutane 139, sai Barno mai 113, Katsina na da 80, Kogi 17, Nasarawa 13, Taraba 10, Benue 9 sai kuma Ebonyi mai 8.

Sauran sun hada da Zamfara mai mutane 7, Plateau 5, Edo da Akwa Ibom da Lagos na da bibiyu, sai kuma Jihohin Oyo da Imo da Rivers da Cross Rivers da Ogun da Bayelsa da Delta da kuma Kebbi dake da guda-guda.



Rahoto
NIGERIA – Rashin aiki a Najeriya ya kai kaso 27.1 a tsakanin watanni 6


Hukumar kididdig ta Najeriya ta fitar da sanarwar samun karuwar marasa aikin yi daga kashi 23.1 zuwa kashi 27.1 a watanni 6 na farkon shekarar nan.

Bayanan da hukumar ta fitar ya nuna cewa yanzu haka jihar Kano ke matsayin ta biyu a jerin jihohin da ke da yawan marasa aikin yi a Najeriya wadanda galibin shekarunsu ya fara daga 15 zuwa 60 .
Alkaluman hukumar kididdigar sun nuna cewa jihar ta Kano na da jumullar mutane miliyan 1 da dubu dari 4 da 20 galibinsu matasa ne da basu da aikin yi.

Yanzu haka dai Najeriyar na da alkaluman mutane miliyan 21 da dubu 764 da 617 wadanda basu da aiki.



-
Labarai1 week ago
Da Ɗumi-Ɗumi A Na zargin Bam Ya Tashi a Unguwar Sabon Gari A Kano Yanzu
-
Labaran jiha1 week ago
Ƴan Bindiga Sun Hallaka Mutane Shida Sun Tafi Da Sarkin Garin Ƙarfi Dake Jihar Kano
-
Labarai2 weeks ago
ASUU Ta Janye Yajin Aikin Da Ta Ke Yi
-
Labarai2 weeks ago
INEC Ta Sanar Da Ranar Rufe Yin Rijistar Katin Zaɓe
-
Labarai4 days ago
Za’a Daina Anfani Da Kuɗin Takarda A Najeriya – CBN
-
Labarai6 days ago
Sabuwar Ƙungiyar Ta’addanci Ta Ɓulla A Kaduna
-
Labarai2 weeks ago
An Rufe Makaranta Bayan Ƙone Ɗaliba Da Ranta Bisa Ɓatanci Ga Annabi A Sokoto
-
Labarai2 weeks ago
Jihohi 32 A Najeriya Na Iya Fuskantar Mummunar Ambaliyar Ruwan Sama A Bana