Sarkin Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero ya sauke Wasu hakiman Dake karkashin masarautar Bichi.

Wanda kuma ya maye gurbinsu da wasu nan take.
Hakiman Da aka sauke Wanda basu yi Mubayi’a ba Sune kamar Haka :-

Hakimin Bichi
Danbatta
Dawakin tofa
Munjibir
Tsanyawa

Bayan da Majalisar masarautar ta Maye Gurbin su da Sababbin Hakiman da suka hada da
1.Abdulhamid Ado Bayero Hakimin Bichi
2.Ma,awuya Abbas Sanusi Hakimin Tsanyawa
3.Dr Abdullahi Maikano Rabi’u Dawakin tofa
4.Alhaji Wada Ibrahim Hakiman Danbatta
5.Alhaji Labaran Abdullahi Hakimin Makoda
6.Malam Isma’il Sarkin Fulani Hakimin Munjibir
Kuma Dukkanin Wadan nan Hakiman aikin su ya fara nan take.
Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ne ya kirkiro sabbin masarautu guda hudu a jihar Kano.